WASHINGTON, DC —
'Yan Najeriya sun soma tofa albarkacin bakinsu game da taron kasa da yadda suke ganin wakilan da gwamnati ta tara a Abuja.
Daga jihar Adamawa, daya daga cikin jihohi uku na arewa maso gabashin kasar dake cikin dokar ta baci, mutane sun bayyana ra'ayoyinsu.
Gyang Sam yace wakilan su je kowa yayi anfani da zuciyarsa ya tabbatar ya aiwatar da gaskiya. Yace duk wanda yayi abun da ba daidai ba "Allah Ya isa" Shi ma Hidus Livinus yace a yi magana bisa gaskiya domin babu wani da zai ce yana jin dadi a kasar. Shi kuma Umar Dankano yace taron shirme ne domin akwai 'yan majalisu da aka zaba. Yace to me yakamata wakilan da aka zaba su yi? Yace barnar kudi ne kawai da rashin makomar Nageriya.
Muhammed Ismail yace taron na zuwa shan shayi ne kawai. Yace menene abu sabo da zasu yi da basu yi da can ba?
Dr. Umar Ardo na jam'iyyar PDP yace ba "girin-girin ba dai ta yi mai domin a ganinsa akwai wata manufa da ake son cimma a karkashin taron. Sabili da kada mutane su dogara da taron domin ba zai kulla komi ba.
Wani batu da ake zaton taron ka iya tabowa shi ne batun sauya akalar shirya zaben da INEC zata shirya a 2015. Amma jami'an hukumar na gani lamari ne maiwuya. Barrister Kasumu Na Geidam shi ne kwamishanan labaru na hukumar a jihar Adamawa yace mutane su sa hankali. Duk wani abun da tayi suna cikin dokar da ta kafata domin babu wanda zai iya canza jadawalinta. Yace mutane su lura wakilan taron mashawarta ne. Babu su a tsarin shari'a ko a rubuce a kundun tsarin mulki na kasar. A sha'ariyance basu da wata matsaya balantan madora. Bayan sun kammala taron zasu tara shawarwarinsu kana su mikawa shugaban kasa. Shi kuma zai duba ya tsinci abubuwan da yake so kana ya turawa majalisun kasa su yi aiki da shi. Shirin zaben INEC babu mai tabashi a shri'ance saidai majalisu na tarayya da kuma na jihohi. Yace layin taron kasa daban layin INEC daban. Babu abun da ya hadasu.
Babu abun da ya raba wakilan taron da mashawartan shugaban kasa domin shi ya nadasu. Wadanda jama'a suka zaba su ne ke da hakin canza dokokin zabe ko kuma yin wasu sabbi.
Wakilan zasu kwashe watanni uku suna muhawara. Daga bisani kuma zasu mikawa shugaban kasa rahotonsu. Shi kuma zai duba ya tsinci abun da yake so kana ya mikawa majalisun tarayya.
Ga karin bayani.