Abdulhamid El Wazir yace cikin abubuwa da dama ya fi kaunar abubuwa biyu wato gyarawa da inganta harkar tsaro a kasar. Ita kuma Adama Shehu Kontagora tace a tattauna kada a kuskura a raba Najeriya. Tace 'yan Najeriya a dunkule a zama daya. Idan kuma za'a yi zabe a tsaya tsakani da Allah a yi adalci. A daina aringijen kuri'u.
Tsohon gwamnan jihar Kano Kanal Sani Bello mai ritaya yace duk wata magana da za'a yi idan babu zaman lafiya maganar banza ce. Yakamata a ba jami'an tsaro iko su yi aikinsu yadda ya kamata a kuma kula da su.
Shi ma tsohon mataimakin sifeton 'yansanda Sanata Nuhu Aliyu bayan yace harkar tsaro nada mahimmanci kuma ya kamata a yi duk abun da yakamata a yi domin a inganta tsaro amma yace taron ba zai yi tasiri ba har sai an hada da majalisun tarayya. Majalisun kasa ne zasu iya kafa dokoki da zasu tabbatar da abubuwan da aka cimma a taron. Ya yi kakausar lafazi kan tabarbarewar harkar tsaro kamar yadda abun da ya faru a Katsina ya nuna. Yace a halin da kasar ke ciki yanzu an wuce barin komi a hannun gwamnatin tarayya.
Ga karin bayani