Tsadar Rayuwa A Birnin Abujan Najeriya

Baraguzen ginin da ya rushe a Abuja

An dade ana kuna cewa rayuwa nada tsada a birnin Abuja musamman gidajen zama. To ko menene musababin hakan?
Birnn Abuja babban birnin Najeriya na daya daga cikin biranen da suka fi tsadar zama. Gidajen haya basa tabuwa musamman ga masu karamin albashi ko karamin karfi.

Tsadar rayuwa a Abuja bata misaltuwa da wasu yankunan Najeriya. Misali kudin hayar gida mai dakuna biyu da mutum zai biya na shekara daya ka iya gina kwatankwacin wannan gidan a wasu sassa a Najeriya. Barazanar rushe gidajen da ba'a gina kan ka'ida a birnin da ministan birnin ya yi, wajen 100,000 da ya ce ya gano, bai canza komi ba, musamman ga masu karamin karfi. A gaskiya ma barazanar ta saka zullumi a cikin wadanda ke rakubewa cikin irin gine-ginen daga inda suke zuwa neman abun rayuwa. Irinsu ne idan gari ya waye su fice daga gidajen, wasu ma ba'a gama ginasu ba, su je cirani ko ma cidamina kana su dawo da dare su kwanta.

Wasu kamfanoni dake gina gidaje su sayar haya ko su sayar sukan fuskaci kutse daga wurin masu uwa a murhu da sukan hana wasu wuraren mallakar makarantu, masallaci, da mijami'a. Irin wadannan kamfanonin sukan karbo lamuni daga bankuna lamarin da kan sa gidajen su kara tsada. Dalili ke nan da wasu ma'akatan ke samun kansu a wasu unguwanni a bayan gari domin neman gidajen haya daidai da karfinsu. Wasu ma sukan zauna a wasu jihohi dake makwataka da Abuja suna zuwa aiki cikin birnin kullum. Alhaji Maje Usman na Unity Garden na cikin wadanda ke gina irin wadannan gidajen inda wani zubin sukan kare a kotu domin kasa gama ginin cikin shekara biyu.

Alhaji Usman ya ce ana son mutane su zo su saka jari a Abuja to amma akwai matsaloli. Misali ma'akaci na iya ranto kudi a gina masa gida, wani kuma kila a banki ya ciwo bashi. Ana cikin ginin sai wani ya zo da takarda daga kotu da ta hana cigaba da ginin. Ko kuma wani babban mutum sai ya yi waya daga wani wuri ya hana aikin ginin.Ya ce ire-ieren wadannan abubuwa ke tayarda hankali.

To ko menene majalisar kasar Najeriya ke yi game da lamarin. Wani dan majalisa Kamisu Ahmed Mailantarki ya ce abun dake rafuwa kamar cuta ce dake damun mutum. Dole sai an yi bincike a san abun dake faruwa kafin a dauki mataki.

Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani


Your browser doesn’t support HTML5

Tsadar Rayuwa A Birnin Abujan Najeriya - 3:15