A cikin rahoton da bankin ya fitar, ya nuna cewa, tun a shekara ta dubu biyu da tara ne Najeriya ta fara aiwatar da tsare tsaren da suka taimaka wajen samar da yanayin da ke habaka kananan masana’antu da suka hada da samar da rance.
Rahoton yace Najeriya na daya daga cikin kasashe goma a duniya da aka sami ci gaba ainun a fannin samar da rance ga kananan masana’antu. Wakilin Sashen Hausa ladan Ibrahim Ayawa ya hada rahoto a kan wannan ci gaban