Matashin yayi magana kan yadda ake kawo musu makamai a kan babura, da yadda ake nuna musu yadda ake warwarewa da hada bindigar, da kuma harba ta. Sannan yayi magana kan yadda suke samun kayan sarki na soja da suke sanyawa.
Haka kuma, ya tabo batun matan da aka ce 'yan kungiyar na kamawa, da yadda suke tafiya da makanikai in zasu kai hari domin sata ko kwace motoci.
Sannan kuma ya ce a yanzu soja da 'yan sanda ba su ne manyan abokan gabar 'ya'yan kungiyar dake warwatse ba.
Ga kashi na biyu na tattaunawar da Haruna Dauda yayi da shi.