Trump Yayi Zargin Mummunar Barazana A Kan Rayuwarsa Daga Kasar Iran

Trump-Zaben 2024

A yau Laraba, tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewar rayuwarsa na fuskantar barazana daga kasar Iran bayan da tawagar yakin neman zaben jam’iyyar Republican ta ce jami’an leken asirin Amurka sun gargade shi game da barazana ta zahiri da ta takaita a kansa daga birnin Tehran

A sanarwar data fitar a yau Talata, tawagar yakin neman zaben Trump tace Amurka ta samu bayanan sirri dake gargadin cewar akwai barazanar zahiri daga kasar Iran ta hallaka Trump.

Har yanzu ba a fayyace ko barazanar da tawagar neman zaben da shi Trump din kansa ke magana a kai sabuwa ce ko kuma wacce aka taba ba da rahotonta a baya ce.

Tawagar neman zaben ba ta yi karin bayani a kan wannan ikrari ba, wanda ke zuwa a dai dai lokacin da shugabannin duniya ke kokarin lalubo hanyar da za a hana rikicin kungiyar Hizbullahi mai samun goyon bayan Iran da Isra’ila kazancewa zuwa yakin da zai mamaye yankin Gabas ta Tsakiya.

Iran dai ta musanta zargin cewar tana kokarin hallaka Trump a wannan bazara, jim kadan bayan da wani dan bindiga ya bude wuta a wani gangami a Pennsylvania, inda ya hallaka mutum guda tare da raunata dan takarar shugaban kasar.