Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tuhumi Mutumin Da Ya Yi Yunkurin Hallaka Trump


Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump a Las Vegas
Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump a Las Vegas

Ryan Wesley Routh, mai shekaru 58, ya bayyana a karon farko a kotun tarayya da ke West Palm Beach, Florida, a ranar Litinin.

An tuhumi mutumin da ya yi yunkurin kashe tsohon Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Lahadi da laifin mallakar bindiga.

Ryan Wesley Routh, mai shekaru 58, ya bayyana a karon farko a kotun tarayya da ke West Palm Beach, Florida, a ranar Litinin.

Bincike daban-daban sun nuna cewa Routh ya shafe mafi yawan rayuwarsa ta girma yana zaune a jihar North Carolina, wata jiha mai bakin teku a tsakiyar yammacin Amurka,

A baya-bayan nan ya zauna a jihar tsibirin Hawaii da ke cikin tekun Pacific, a karamar unguwar bakin teku ta Kaaawa, inda shi da dansa suke gudanar da kamfanin gina rumfuna, bisa ga wani shafin yanar gizo da aka adana na kasuwancin.

Rahotanni a Amurka sun ce Routh ya sha yin arangama da 'yan sanda yayin da yake zaune a Greensboro, North Carolina.

An same shi da laifin mallakar makamin kare-dangi a shekarar 2002, bayan da aka tsayar da shi a wani binciken 'yan sanda a kan hanya, sannan ya kulle kansa a cikin rufin wurin kasuwancin da ya mallaka, a cewar rahotanni.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi Allah wadai da yunkurin kisa na biyu da ake zargin an kai wa Trump, yana mai cewa irin wannan hallaya ba ta da alaka da Amurkawa.

“Babu gurbi ga tashin hankalin siyasa a Amurka. Babu. Sifili. Babu ko da yaushe,” in ji Biden a wani taron jami’o’in tarihi na bakaken fata (HBCU) da aka gudanar a Philadelphia.

“A Amurka, muna warware sabaninmu cikin lumana ta hanyar zabe. Ba tare da amfani da bindiga ba,” Biden ya ce a ranar Litinin

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG