Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Na Laluben Dalilin Yunkurin Kashe Trump


Donald Trump
Donald Trump

Jami’ai sun ce bayanan da aka samu daga wayar Routh sun nuna cewa ya boya tsawon sa’o’i 12, yana cikin wasu shuke-shuke a bakin katangar waya da ke tsakanin rami na biyar da na bakwai na filin wasan golf.

Masu bincike na Amurka suna nazarin asusun kafofin sada zumunta da sauran wallafe-wallafen wanda ake zargi da yunkurin kashe tsohon Shugaban Kasa Donald Trump a ranar Lahadi, suna kokarin gano dalilin yunkurin da kuma yiwuwar akwai wasu da suka taka rawa a wannan al’amari.

‘Yan sanda a Florida sun kama Ryan Wesley Routh mai shekaru 58, inda suka tare shi a kan wata babbar hanya ranar Lahadi, kimanin awa guda bayan ya gudu daga Trump International Golf Club na tsohon shugaban kasar da ke West Palm Beach, Florida.

Jami’ai sun ce bayanan da aka samu daga wayar Routh sun nuna cewa ya boye tsawon sa’o’i 12, yana cikin wasu shuke-shuke a bakin katangar waya da ke tsakanin rami na biyar da na bakwai na filin wasan golf.

An tuhumi Routh da laifin mallakar bindiga duk da kasancewarsa tsohon mai laifi, da kuma mallakar bindiga mai lamban da aka shafe.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG