Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya zabi Sanata James David Vance na jihar Ohio a matsayin mataimakinsa a takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Republican kamar yadda AP ya ruwaito.
A ranar Litinin Trump mai shekaru 78 ya zabi Vance mai shekaru 39 a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2024 wanda za a yi a ranar 5 ga watan Nuwamba.
Baya ga shi Vance, a baya, an bayyana mutum biyu da ake tunanin Trump zai dauka ciki har da Sanata Marco Rubio na jihar Florida da gwamnan jihar North Dakota Doug Burgum.
Trump ya sanar da zabinsa da aka jima ana dako ne a babban taron jam’iyyar Republican na kasa da aka fara a Milwaukee da ke jihar Winsconsin.
Dukkan wakilan da suka halarci babban taron na ‘yan Republican daga jihohin Amurka sun jaddada Trump a matsayin dan takararsu a zaben shugaban kasa inda ya samu wakilai sama da 1,215 adadin da ake bukata dan takara ya samu.
Gangamin na ‘yan Republican na zuwa ne kwanaki biyu bayan da Trump ya tsallake rijiya da baya inda wani dan bindiga ya yi yunkurin halaka shi yayin gangamin yakin neman zabe a Pennsylvania a ranar Asabar.
An haifi Vance ne a garin Middleton da ke jihar Ohio a ranar 2 ga watan Agustan 1984.
Ya kammala karatun lauyansa a makarantar koyon aikin lauya ta Yale, ya kuma taba aiki da rundunar sojin Amurka bayan da ya kammala karatun sakandare.
An fara zaben Vance a matsayin sanata ne a shekarar 2022 bayan da ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar Democrat Tim Ryan.
A shekarar 2016, ya kasance daya daga cikin masu sukar Trump, amma ya sauya akalar kalamansa a lokacin da ya tashi yin takararsa ta farko a shekarar 2022.
Sunan matarsa Usha Vance kuma sun yi aure ne a shekarar 2014. Suna da ‘ya’ya uku: Ewan, Vivek da Mirabel.