Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Mika Sakon Jajensa Ga Donald Trump

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (Hoto: Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (Hoto: Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

A sanarwar da mai magana da yawun Shugaba Tinubun, Ajuri Ngelale ya fitar, yace “harin da aka kai wa tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, abu ne mai kyama kuma ya wuce kololuwar ka'idojin dimokradiyya.

A yayin da Shuwagabannin ƙasashen duniya ke mayar da martani da kuma mika saƙon jajen su ga tsohon shugaban Amurka kuma dan takarar jam'iyyan Republican, Donald Trump wanda ya gamu da harbin bindiga, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya mika nasa jaje.

A sanarwar da mai magana da yawun Shugaba Tinubun, Ajuri Ngelale ya fitar, yace “harin da aka kai wa tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, abu ne mai kyama kuma ya wuce kololuwar ka'idojin dimokradiyya.

“Ina mika ta'aziyyata ga tsohon shugaban kasar da fatan samun sauki.

“Ina kuma jajantawa iyalan wadanda suka rasu da wadanda suka jikkata da fatan Allah ya basu lafiya.

"Najeriya na tare da Amurka a wannan lokaci” inji shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG