Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Kori Karar Da Aka Shigar Da Trump Kan Wasu Takardun Sirri Da Ake Zargin Ya Boye


Tsohon hoto: Donald Trump, hagu, da mai shigar da kara Jack Smith, dama
Tsohon hoto: Donald Trump, hagu, da mai shigar da kara Jack Smith, dama

Hukuncin na zuwa ne kwana biyu bayan da Trump ya tsallake rijiya da baya a lokacin da wani dan bindiga ya yi yunkurin halaka shi.

Wani alkalin kotun tarayya a jihar Florida ya kori karar da aka shigar da tsohon shugaban Amurka Donald Trump kan mallakar wasu takardu dauke da bayanan sirrin kasa.

Alkalin ya kori karar ne bayan damuwa da aka nuna kan yadda aka nada mai shigar da kara kan shari’ar.

Lauyoyin Trump sun yi korafin cewa ba a bi ka’ida ba wajen nada lauya Jack Smith kana ba a bin doka wajen kudaden da ma’aikatar shari’a take ba ofishinsa.

A ranar Litinin kotun ta yi fatali da karar.

Wani mai magana da yawun Smith da lauyan Trump sun ki cewa uffan bayan da aka aika musu da sakon tes a cewar Kamfanin Dillacin Labarai na AP.

Wannan mataki da kotun ta dauka na zuwa ne yayin da jam’iyyar adawa ta Republican ta fara babban taronta a Milawaukee da ke jihar Winsconsin.

Ana sa ran za a tabbatarwa da Trump takararsa a taron yayin da ake dakon ya sanar da wanda zai dauka a matsayin mataimaki.

Taron na gudana ne kwana biyu bayan da aka yi yunkurin halaka shi inda wani dan bindiga ya harbe shi a Pennsylvania.

Trump na cikin koshin lafiya amma ya ji rauni a kunnensa.

Jami’ar tsaro sun harbe dan bindigar har lahira, wanda ya kashe mutum daya ya kuma jikkata wani a lokacin harbin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG