A yau Alhamis zababben shugaban Amurka Donald Trump ya kada kararrawar bude kasuwar hada-hadar hannayen jarin birnin New York.
Dan jam’iyyar Republican din ya gina arzikinsa ta hanyar zuba jari a harkar gidaje a birnin New York kafin ya shiga siyasa.
A shekararsa ta farko a matsayin shugaban kasa, ya auna irin nasarar da ya samu a rayuwa da karfin kasuwar hannayen jarin, wacce ta yi maraba da sake zabensa da aka yi.
Kada kararrawar wata alama ce dake nuni da budewa ko rufe hada-hadar yini a babbar kasuwar hannayen jari ta duniya, kuma ana yiwa hakan kallon karramawa.
A tarihi ana kebe wannan al’ada ga shugabannin kamfanonin dake murnar tallata hajarsu ta farko ko kuma wasu nasarori da aka samu a bangaren kamfanoni, sai dai fitattun mutane da ‘yan siyasa irinsu Ronald Reagan da Nelson Mandela da Arnold Schwarzenegger sun taba kada ta suma