Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zababben Shugaban Amurka Donald Trump Yayi Barazana Ga Kungiyar Kawance Ta BRICS


Zababben shugaban Amurka Donald Trump
Zababben shugaban Amurka Donald Trump

A ranar Asabar zababben shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar aza harajin kashi 100 kan gungun kasashen BRICS 9  muddin suka yi gigin yin kafar angulu ga dalar Amurka.

A ranar Asabar zababben shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar aza harajin kashi 100 kan gungun kasashen BRICS 9 muddin suka yi gigin yin kafar angulu ga dalar Amurka.

Barazanar ta sa dai na kaikaitar kasashen nan ne na kungiyar kawance da ake kira BRICS da ta kunshi kasashen Brazil, Russia,India, China, South Africa, Egypt, Ethiopia, Iran da hadaddiyar daular larabawa.

Kasashen Turkiyya da Azerbaijan da Malaysia ma sun aike da bukatar zama mambobin kungiyar kawancen, yayinda sauran kasashe da dama sun bayyana sha’ar ba za’a bar su a baya ba.

Yayin da dalar Amurka tayi fintinkau a kudin da akafi amfani da su a duk wata harkar kasuwanci a duniya, da ta sha tsallake duk wani kalubale kan alkadarin ta, manbobin kungiyar kawancen ta BRICS dama sauran kasashe masu tasowa sunce, sun gaji da babakeren da dalar Amurka tayi a tsarin kudin hadahada a duniya.

Trump ya fada ta wallafar da yayi a shafin sa, inda yace,’ muna bukatar tabbaci daga kasashen cewa, ba zasu kirkiro wani sabon kudi na BRICS ba, kuma ba zasu sake su marawa wani kudi baya ba domin maye karkarfar dalar Amurka, in ko ba haka bas u fuskanci harajin kashi 100, su kuma shirya yin sallama da sayar da wani abu ga kyakkyawan tattalin arzikin Amurka.’’

A wani babban taron kasashen BRICS da aka gudanar a watan Oktoba, shugaban Rasha Vladimir Putin ya zargi Amurka da yin amfani da Dala a matsayin makami, inda ya bayyana hakan a matsayin babban kuskure.

A lokacin Putin yace, ba mu ne muka ki amfani da dala ba, to amma idan basa son su kyale mu muyi auki, ya zamu yi kenan? Yace don haka dole ne mu nemi abinda zai fishshe mu.

Musamman Rasha ta aza kaimi wajen samar da sabon tsarin amfani da kudade, da zai samar da wata dama ta tafiyar da aiyyukan banki a duniyar hadahadar kudi, da zai ba Rasha damar kaucewa takunkuman kasashen yammaci, ta kuma gudanar da kasuwanci da sauran kasashe.

Trump yace ba yadda za’ayi BRICS ta maye gurbin dalar Amurka a kasuwancin duniya, kuma duk kasar da tayi gigin tabbatar da hakan, to ta shirya yin adabo da Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG