Trump Ya Dora Laifin Rikicin Da Ya Faru A Charlottesville Akan Bangarori Biyu

Trump yayi sabon furucin ne a zauren ofishinsa dake birnin New York jiya Talata, inda ya yi jawabi akan sake gina kayayyakin more rayuwa a Amurka.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake komawa akan batun dora laifi kan bangarori biyu a rikicin nuna wariyar launin fata da ya auku ranar Asabar din da ta gabata a garin Charlottesville dake jihar Virginia, bayan jawabin da yayi ranar Litinin, inda ya yi Allah Wadai da turawa masu kyamar launin fata, amma bai ambaci wadanda suka yi zanga-zangar rashin amincewa da masu kyamar launin fatar ba.

Ba tare da bata lokaci ba taron manema labaran da akayi ya koma na tada jijiyar wuya tsakanin shugaban da ‘yan jarida dake so su san dalilin da ya sa sai da aka yi kwanaki biyu kafin shugaban yayi amfani da kalmar Neo-Nazis da Ku Klux Klan da kuma turawa masu tsattsauran ra’ayin kyamar launin fata.

A wani lamari dabam kuma, shugaba Donald Trump yace shugabannin manyan kamfanonin da suka fice daga kwamitin daya kafa na bayar da shawarwari akan masana’antu sun fice ne saboda kunya ganin yadda suke sarrafa abubuwa a kasashen waje.

Trump ya fadawa manema labarai a birnin New York cewa shugabannin manyan kamfanonin basa daukar aikinsu da muhimmanci idan aka zo ga kayayyakin da ake sarrafawa a gida Amurka.

Trump ya kara da cewa, ya sha nuna masu abinda yake gani ya kamata a yi don maido da masana’antu Amurka.