Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi hasashen cewa, karshenta takaddamar yunkurin tsige shi da ‘yan majalisar wakilai na bangaren ‘yan jam’iyyar Democrat ke yi, ta kare a gaban kotun kolin kasar.
A jiya Laraba, Shugaba Trump ya fadawa manema labarai hakan, kwana guda bayan da Fadar gwamnati ta White House, ta yi kememe ta ce ba za ta sa hannu a binciken ba, domin ba shi da hurumi a kundin tsarin mulkin kasar.
Ko da yake Shugaban na Amurka ya nuna kwarin gwiwar cewa ‘yan jam’iyyarsa ba za su ba shi kunya ba.
“Idan aka kai matakin da batun zai je gaban majalisar dattawa, za mu samu nasara, kawunan ‘yan jam’iyyar Republican a hade suke sosai, wannan shi ne babban bita-da-kulli da muka taba gani a tarihin kasarmu.” In ji shugaba Trump.
Duk da cewa Trump bai fadi takamaimai abin da yake so ‘yan Democrat din su yi ba, amma a baya ya ce zai ba su hadin kai “idan aka ba ‘yan Republican hakkokinsu.”