Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Samun Wani Jami’in Leken Asirin Amurka Mai kwarmato


Joe Biden da dansa Hunter
Joe Biden da dansa Hunter

An sake samun wani jami’in leken asirin Amurka mai kwarmata bayanai da ya fito fili ya bayyana damuwarsa akan tattaunawa ta wayar tarho da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi da shugaban Ukraine Volodymyr Zeleskiy.

Wani lauya mai suna Mark Zaid, wanda ke wakilitar masu kwarmata bayanan duka biyu, ya tabbatar da labarin bullar mai kwarmato na biyu din ga Muryar Amurka.

Zaid ya ce sabon mai kwarmata bayanan ya na da, abin da lauyan ya kira, “masaniya ta ainihi” game da tattaunawa ta wayar tarho din da aka yi da Trump, wanda hakan ke tabbatar da ainihin korafin mai kwarmato na farko na cewa Trump ya bukaci gwamnatin wata kasar waje da ta kwakulo wata tabargaza game da dan takarar shugaban kasa a shekarar 2020, Joe Biden.

Kafin wannan lokacin, Trump na korafin cewa mai kwarmato na farko ya gabatar da abin da ya jiyo ne daga wadanda su ma jiyowa su ka yi game da wayar tarho din da Trump ya buga ma Zeleskiy. Kiran ya nuna Trump na gaya wa Zelenskiy da ya binciki zargin aikata almundahana a Ukraine da ake ma Biden da dansa Hunter, lamarin da ya janyo kafa kwamitin binciken yiwuwar tsige Trump da Majalisar Wakilan Amurka mai rinjayen 'yan Demokarat ta yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG