Lauyan White House Pat Cipollone ya aike da wata wasika mai shafi takwas ga shugabannin jami’iyar Democrats a majalisa, ciki har da kakakin majalisar Nanacy Pelosi, da suke bincike a kan ko Trump ya take doka da ya nemi Ukraine ta gudanar da bincike a kan dan takarar Democrats Joe Biden.
Cipollone ya zargi Democrats da rashin adalci da kuma sabawa tsarin kundin mulkin kasa.
Yace suna hana shugaba Trump ya yiwa wanda ya bankado batun tambayoyi domin ya ga shaidar da zasu gudanar da binciken akai ko za tsige shi.
Pelosi ta maida martani ga fadar White House da yammacin jiya Talata, tana kiran wasikar kuskure, lamarin da tace wani sabon yunkuri na rufe cin amanar da Trump ya yiwa Democrats da kuma nuna shugaban kasar yafi karfin doka.
Facebook Forum