Shugaban Amurka da jami’an gwamnatinsa za su gana a yau Asabar, game da guguwar Irma wacce aka yi hasashen za ta isa jihar Florida a karshen makon nan, wacce kuma ta halaka akalla mutum 21 a yankin Carribea da ta ratsa, tare da haddasa mummunar barna.
A jiya Juma’a shugaba Donald Trump yayin wata ganawa da manema labarai a Fadar White House, ya ba da kwarin gwiwar cewa komai zai tafi daidai, gabanin ya kama hanyarsa ta zuwa Camp David, inda zai yi taron da jami’an gwamnatin tasa.
Mai ba da shawara kan harkokin tsaron cikin gida a Fadar ta White Tom Bossert, ya yi kira ga mutane da su kula da kansu, domin ta haka ne kadai za su iya kula da wasu.
Yayin da aka tambaye shi, mai ya fi bashi tsoro dangane da wannan guguwar, sai ya ce, yafi fargabar karancin man fetur da za a iya fuskanta, lura da cewa kusan biyar zuwa shida na matatun man da ke jihar Texas duk a rufe suke, sanadiyar guguwar Harvey da aka fuskanta a baya.s
Hukumar ba da agajin gaggawa ta FEMA, ta ce tuni ta tanadi abinci, da barguna da magunguna da kuma kayayyakin bukatu na kananan yara.