Shugaba Donald Trump yace zai waiwayi shawarar daya yanke ta kawo karshen shirin kare Yara yayan bakin haure marasa izinin zama kusan dubu 800,000 kaucewa maida su kasashen su idan yan majalisa basu yi wani abu akan lamarin ba.
Sa’o’i bayan Jami’an gwamnati sun ce baza a kara karbar takardar shiga cikin shirin na DACA ba, Trump ya rubuta a twitter a yammacin Talata cewa “Yan majalisa na da watanni shida su halatta DACA (Wani abu da gwamnatin Obama ta kasa yi). Idan sun kasa yace zai sake waiwayar lamarin!”
Masu zanga zangar nuna rashin amincewa wannan mataki sun taru a biranen Washington da Los Angeles da New York da kuma Denver da sauran birane.
Wani d'an raji mai suna Gustavo Torres ya shaidawa taron jama’a a gaban White House cewa: “Wannan shugaban kasar yayi wa al’ummar mu karya… Ya fada mana yana kaunar mu masu burin wato Dreamers.’ Amma yayi mana karya a saboda haka shi Makaryacine!”
Facebook Forum