Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Sake Kai Ziyara Texas


Lokacin ziyarar farko da Trump da uwargidansa Melania suka kai jihar Texas. Nan a filin tashin jiragen Corpus Christi ne ranar 29, ga watan Agusta 2017.
Lokacin ziyarar farko da Trump da uwargidansa Melania suka kai jihar Texas. Nan a filin tashin jiragen Corpus Christi ne ranar 29, ga watan Agusta 2017.

A karo na biyu cikin mako guda, shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa, Melania Trump za su sake kai ziyara jihar Texas domin jajintawa mutane da kuma ganewa idununsu yadda guguwar Harvey ta yi barna a yankin.

Yayin da yake shirin kai ziyara birnin Houston da ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Texas, shugaba Donald Trump ya aika da wasika zuwa majalisar dokokin Amurka, yana neman kusan Dala biliyan 8, wadanda za a yi amfani da su domin tallafawa jihohin Texas da Louisiana.

Ana sa ran, wannan bukata da shugaban ya gabatar wani kaso ne na farko da ya hada da Dala biliyan 7.4 da za a ba hukumar ba da agajin gaggawa ta tarayya, wacce kudadenta ke karewa a hankali, sannan Dala miliyan 450 kuma, za a baiwa masu kananan masana’antu bashi domin su fara watstsakewa daga wannan balai’in da ya same su.

A yau Asabar ake sa ran shugaba Trump da uwargindansa Melania Trump za su kai ziyara birnin na Houston tare da yada zango a yankin Lake Charles da kuma Louisiana, wadanda su ma bala’in guguwar ya shafa, domin ya gana da wadanda lamarin ya rutsa da su, ya kuma ganewa idonsa irin barnar da guguwar ta yi

Wannan ziyara za ta kasance ita ce ta biyu, da shugaba Trump zai kai tun bayan aukuwar ambaliyar ruwan.

A daya bangaren kuma, masu ayyukan ceto na can suna ci gaba da neman wadanda suka tsira da ransu sama da mako guda, bayan da guguwar ta Harvey ta ratsa ta gabar tekun Gulf dake jihar Texas, inda ta zub da ruwan sama kamar da bakin kwarya, sannan ta raba mutane sama da miliyan daya da muhallansu, ta kuma salwantar da rayuka 39.

Yayin da ruwan da ya malale wasu sassan jihar ta Texas ya fara sauka, wadanda Allah ya yiwa gyadar dogo, sun fara komawa gidajensu domin su auna irin barnar da guguwar ta yi musu.

Sai dai duk da cewa ruwan da ya taru yana raguwa, hukumomin jihar sun yi gargadi ga jama’a cewa akwai yiwuwar samun barazana ga ruyuwa a wasu kogunan da ruwan mamaye.

A jiya Juma’a, jami’a a birnin Houston sun ce gidaje dubu 156 ne suka salwanta a karamar hukumar Harris, wacce ta hada har da Houston, birni na hudu da ya fi yawan jama’a a nan Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG