Trump dan takarar Republican yana kara caccakar Hillary Clinton

Hillary Clinton 'yar Democrta da Donald Trump dan Republican

Donald Trump wanda bisa duka alamu shi ne zai zama dan takarar shugaban kasar Amurka a karkashin jam'iyyar Republican ya soma caccakar Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrats wadda yake kyautata zaton da ita zai kara a zaben da za'a yi watan Nuwamba

Yayinda yake cigaba da fafutikar neman zabe a yankin Pacific da jihar Washington, Trump caccaki Hillary Clinton da mijinta tsohon shugaban kasar wato, Bill Clinton.

Yace ta auri Bill Clinton mutumin da shi ne ya fi kowa cin mutuncin mata a tarihin siyasar kasar. Yace ta auri mutumin da ya jima mata. Idan kuma aka yi la'akari sosai ita ma tana jima mata, inji Trump.

Wannan babatun da Trump yake yi kan Hillary shi ne mafi muni tunda suka fara neman zabe. To saidai Clinton bata fara fitowa barobaro ba ta caccakeshi amma tana yi masa sheganta da wayo.

Hillary tace " idan na yi tunanen abun dake faruwa koda ma bana takarar zan yi duk iyakacin kokarina na tabbatar wannan dan da yaki girma na jam'iyyar Republican bai yi kusa da Fadar White House.

Magoya bayanta sun ji dadin yadda ta mayarwa Trump martani amma sun ce nan gaba dole ta yi mashi fito na fito.

Trump mai kalamun batanci