Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Ja’afaru Isa, shugaban hukumar kula da Almajirai da ilimin yaran da ba su zuwa makaranta yayin da Dr Idris Sani zai zama Babban Sakatare, kamar yadda da Cif Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.
Ya ce Ja’afar-Isa shugaba ne da ake girmamawa kuma a baya ya yi aiki a matsayin tsohon gwamnan Kaduna daga 1993- 1996.
Shugaban ya kuma amince da nadin Tijjani Abbas a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin masarautu.
“Shugaban kasa yana sa ran sabbin wadanda aka nada za su yi amfani da kwarewar da suke da ita wajen gudanar da wannan muhimmin kwamiti, wanda ke tasiri a cikin al’umma.