abuja, nigeria —
Sabon shirin arewa a yau ya ci gaba da duba batun dokar kafa hukumar kula da almajirai da tsohuwar gwamnatin Buhari ta sanya wa hannu a jajiberin sauka daga mulki. Sannan kuma shirin zai kammala da batun matakan kula da daliban jihar Yobe da su ka dawo daga Sudan.
Dan majalisar dokoki Shehu Balarabe Kakale daga Sokoto, shi ne ya jagoranci tsarawa da samar da dokar da ta samu sanya hannun tsohon shugaba Buhari.
Mai kula da tura dalibai daga Yobe karatu a kasashen Larabawa Malam Umar Abubakar, ya ci gaba da yin bayani kan bin kadin daliban da rikicin Sudan ya tilasta su ka dawo gida, inda ya karfafa muhimmancin samun ilimi don yaki da tsattsauran ra’ayi da ka iya kaiwa ga ta’addanci.
Saurari cikakken shirin cikin sauti: