Gwamnatin ta soma aiki domin amfani da wani tsari na kasar Indonesia da ke hana yara bara lokacin da suke neman ilimi wanda kuma zai kawar da su daga tituna.
Matsalar yawaitar yara da ke gararamba a tituna ta jima tana addabar gwamnatoci a Najeriya musamman na arewa inda matsalar tafi kamari.
Wannan ne ya sa gwamnatoci da ma hukumomin dake bayar da tallafi na kasashen duniya ke fadi-tashi wajen shawo kan wannan matsalar, kamar wani yunkuri da gwamnatin Sakkwato ta yi na samar da tsarin doka wajen magance ta.
Da yake tsokaci a kan shirin, Dokta Umar Altine Dandin Mahe shugaban hukumar ilimin larabci da addini musulunci a jihar Sokoto, kuma jagoran aiwatar shirin, yace shirin ya kunshi koyar da yara karatun boko da na addini da koyar da sana'o'i lokaci daya.
Bayan shafe tsawon lokaci ana aiki akan wannan tsarin karshe an samar da daftarin da zai yi jagora ga aikin, wanda gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar tare da sanya hannu ga dokokin hukumomi biyu masu hannu ga aikin da sauran wasu ayukka na daban.
Kafin tattara wannan kundin sai da aka gano adadin makarantun da ake samun irin wadannan yaran, da daliban su suka zarce dubu dari bakwai.
A na shi bayanin, Masanin harkokin ilimi, Dokta Bala Muhammad na jami'ar Bayero ta kano ya ce, idan jihohin arewa za su yi koyi da wannan tsarin za a samu mafita ga matsalar yara dake gararamba a tituna.
Gwamnatoci a Najeriya har ma da hukumomi da ke bayar da tallafi na kasashen duniya sun sha yin fafatuka wajen ganin an samu rage miliyoyin yara da ke gararamba akan tituna lokacin da ya kamata ace suna makaranta, sai dai har yanzu a iya cewa da sauran rina a kaba.
Yanzu dai a iya cewa an samar da gada da za a bi, don maganin wannan matsalar, sai dai yin amfani da tsarin yadda ya kamata ne zai iya nuna nasara ko akasin haka.
Saurari rahoton cikin sauti: