A wata hira da manema labarai bayan ganarwarsa da Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari tare da Bisi Akande, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ahmed Bola Tinubu ya shawarci tsofaffin shugabannin Najeriya Obasanjo da Babangida da su hakura da siyasa su rungumi ritaya da karban kudin fanshonsu.
Asiwaju Bola Tinubu a cewar Daily Trust, yana mayar wa tsofaffin shugabannin martani ne akan kiran da suka yi wa Muhammad Buhari cewa kada ya tsaya takara a shekarar 2019.
"Ba na bin inuwar mutum. Mu bar tsofaffin shugabanninmu su shiga kungiyar wadanda suka yi ritaya su kuma ci gaba da karban fansho dinsu. Amma suna iya shiga siyasa idan har suna sha'awa, duniya ce da kowa ke da 'yanci." Inji Tinubu.
Ya kara da cewa "Amma 'yancin ba na shiga ko ina ba ne barkatai. Amma suna iya barinmu mu ciyar da kasarmu gaba. Wannan shi ne kalubalen duk dan Najeriya."
Idan ba'a manta ba, a kwanan nan, Shugaba Buhari ya nada Bola Tinubu ya jagoranci kwamitin warware rikicin jam'iyyar da ya addabe ta a jihohi da dama domin samun masalaha kafin zaben shekarar 2019, kamar yadda jaridar ta daily Trust ta wallafa.