Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin a Ina Da Ina Tinubu Zai Yi Sulhu a Tsakanin 'Yan Jam'iyyar APC?


Ahmed Bola Ashiwaju Tinubu shugaban kwamitin sulhu
Ahmed Bola Ashiwaju Tinubu shugaban kwamitin sulhu

Rigingimun da suka mamaye jam'iyyar APC da ke mulkin Najeriya sun sa shugaban kasa nada kwamitin neman sulhu a karkashin shugabancin tsohon gwamnan jihar Legas, Ahmed Bola Tinubu, shin a wadanne jihohi ne 'ya'yan jam'iyyar ta APC ba sa jituwa? Karanta wannan labari.

'Yan Najeriya ciki har da masana sun fara tsokaci kan kwamitin sulhu da shugaban Najeriya Muhammadu Buahri ya kafa domin sasanta 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki.

Shugaban ya nada Ahmed Bola Tinubu a matsayin wanda zai shiga tsakanin rigingimun cikin gida da suka addabi jam'iyyar ta APC.

Rikicin da ya fito fili na 'ya'yan jam'iyyar ta APC shi ne na tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamna mai ci a yanzu a Abdullahi Ganduje.

Baya ga wannan rikici na Kano, akwai dumbin 'ya'yan jam'iyyar da ba sa jituwa lamarin da ya kai ga kafa wannan kwamiti.

Saurari wannan rahoton da Babangida Jibril ya aiko mana domin jin sauran 'yan jam'iyyar ta APC da ba sa ga maciji da kuma jin tsokacin da masana suka yi kan kafa wannan kwamiti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG