Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Gaza, Ya Kamata a Kafa Sabuwar Jam’iya – Inji Obasanjo


Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Oabsanjo
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Oabsanjo

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obansanjo, ya ce, shugaba Buhari da manyan jam'iyun kasar, wato APC da PDP, sun gaza kyautata makomar Najeriya, saboda haka, kada ya yi takara a 2019 a kuma kafa sabuwar jam'iya.

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya gaza wajen kawar da matsalolin Najeriya, yana mai cewa lokaci ya yi da zai je ya “huta.”

Obasanjo wanda ya bayyana hakan a wata doguwar rubutacciyar sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya kara da cewa, manyan jam’iyun kasar guda biyu, wato APC da PDP sun gaza, saboda haka a kafa wata sabuwar hadaka, wacce za ta kunshi kowa da kowa mai suna “Coalition For Nigeria” (CN.)

“Muna bukatar wata hadaka, wacce za a kira ta Coalition of Nigeria, hadakar da za ta zama jam’iya ta siyasa a daidai wannan lokaci, wacce za ta kunshi dukkanin ‘yan Najeriya na gari.”

Ya kara da cewa “Idan har aka kai matakin da jam’iyar za ta fitar da dan takara, ni zan ja gefe na ci gaba da zama wanda baya mu’amulla da siyasa kai-tsaye, ya kamata a bude hedkwatar wannan hadaka a Abuja.”

A cikin sanarwar, tsohon shugaban ya nuna gazawar shugaba Buhari yana mai cewa, har yanzu al’amura ba su daidaita ba.

“Irin yanayin da ya sa ‘yan Najeriya suka fita kwansu-da-kwarkwatarsu suka ki zaben dan uwana Jonathan har yanzu ana cikinsa.” In ji Obasanjo.

Dalilin hakan a cewar shi, ya kamata Buhari ya hakura da mulkin Najeriya, ya je ya huta.

“Ina rokon dan uwana Buhari, da ya duba yiwuwar zuwa ya je ya huta a daidai wannan lokaci na rayuwarsa. Ina mai ci gaba da mai fatan koshin lafiya, domin ya mori ritayarsa daga ayyukan al'uma da ya yi, amma ba lallai ba ne Buhari ya karbi shawarata, amma ko ya karba ko kuma akasin haka, akwai bukatar Najeriya ta ci gaba ta nemi makoma mai kyau.”

Koda ya ke, Obansanjo, ya yabi irin kokarin da Buhari ya yi, a fagen yaki da ta’addanci da kuma cin hanci da rashawa, amma ya ce har yanzu "akwai rina a kaba” a wadannan fannonin.

Ya ba da misali a fannin tattalin arzikin kasa, inda ya ce Buhari ya yi kasa a gwiwa, yana mai cewa ana nuna wariya da ‘yan uwantaka da sanayya da kuma saka wasu a rukunin “shafaffu da mai” a fannin bin doka.

A cikin rubutacciyar sanarwar, Obansajo ya kawo misali da batun yadda Buhari ya tafiyar da abin fallasan nan da ya shafi Maina.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG