WASHINGTON, D. C. - Ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris ne ya bayyana haka ranar Talata a Abuja bayan wakilan gwamnati masu tattauna batun sabon albashi sun gana da shugaban kasar.
“Shugaban kasa ya umurci Ministan Kudi da ya yi lissafi, ya gano yadda al’amarin zai kasance cikin kwana biyu, ta yadda za mu samu alkaluman da za mu sake tattaunawa da kungiyar kwadago”, acewar ministan.
Ministan ya kara da cewa “Shugaban kasa ya kuduri yin aiki da duk abin da kwamitin ya amince da shi. Ya kuma duba yadda zai kyautata walwalar ‘yan Najeriya.”
Idris ya kuma ce gwamnati ba ta adawa da karin albashi.
Tawagar gwamnatin tarayya ta hada da Ministan Yada Labaraim Idris, da Ministan Kudi, Edun, da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da Ministan Kwadago Nkiruka Onyejeocha, da Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila; da shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari.
Tun da farko a ranar Talata, kungiyar kwadago ta dakatar da yajin aikin da ta ke yi a fadin kasar wanda ta fara da tsakar daren ranar Litinin bayan ta ki amincewa da tayin naira dubu sittin a matsayin albashi mafi karanci da gwamnati ta yi.