Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Gwamnati Na Goyon Bayan Kungiyar Kwadago Kan Sabon Tsarin Mafi Karancin Albashi


Kungiyar Kwadago A Najeriya
Kungiyar Kwadago A Najeriya

Ma’aikatan gwamnatin Najeriya na marawa kungiyar kwaddago baya da ke neman gwamnatin tarayya ta kara mafi karancin albashi da ga dubu 30 zuwa dubu 400.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya ma'aikata Naira dubu dari 4 a matsayin matsakancin albashi bisa la'akari da tsadar rayuwa yayin da ake samun gagarumin karuwar farashin kayan masarufi, da kudin makaranta da kudin haya da kuma na sufuri

Kungiyar ta ce Ma’aikata ma su zuwa wuraren aiki a kowacce rana, su na daga cikin wadanda suka fi ji a jikinsu yayin da rayuwa ke kara tsananta a Najeriya.

A wata kebabbiyar hira da Muryar Amurka, Sakataren Kudi na NLC, Mohammed Ibrahim yace munin lamarin a yanzu, ya sa kungiyoyin kwadago suke neman gwamnati ta rika biyan ma’aikata albashi mafi karanci kimanin naira dubu 400.

Ya kara da cewa “Idan ka biya jami’in tsaro kudin daya dace yasan kudin zai isa ya kula da iyalinsa dakyau mai zaisa ya kalli Naira biyar Naira goma, Idan ka biya malamin makaranta albashi mai kyau dole zai zauna ya karantar da yayanka- A yanzu Abinda muka fahimta shine wannan shine kwatankancin abinda zai iya sa karamin ma’aikaci ya biya bukatarsa kasa da haka Sai dai a cigaba da tauye hakkin mutane a cigaba da karyar cewa ana yaki da cin hanci.”

A ‘yan kwanakin nan, gwamnatin Najeriyar ta kaddamar da kwamiti da zai duba batun kara albashin ma’aikata – sai dai wasu na gani akwai babban kalubale domin dududu,

Ma’aikatan gwamnatin tarayya ba su wuce 720,000 ba, a kasar dake da mutane kimanin miliyan dari biyu.

Duk da haka amma, wasu ma’aikatan gwamnati na fatan ganin shawarar da kungiyoyin kwadagon suka bayar ta tabbata.

A cewar Saminu Liti Madaki “Da albashina na kaini akalla sati uku amma yanzu baya wuce kwana goma Idan na turawa iyalina su suna Kaduna ni ina Abuja, sauran ragowar kwanakin saidai naci bashi kodai Nasan wasu hanyoyi dazan dinga samu har ya kaini sauran ragowar kwanakin Tabbas karin albashin zaiyi encouraging domin samunka bai karu ba amma dawainiya ta karu so Ko abunda yafi 400,000 a karashi Muna bukata”

Shima Nathaniel Gambo, ma’aikacin gwamnati ne, kuma yace “Akwai damuwoyi da yawa a Najeriya, idan su NLC suka yi nasara, gwamanti ta amince ta biya wannan mafi karancin albashi, zai taimaka mana sosai, Muna fata NlC zasu tabattar an amince a biya wannan kudin domin Muna da damuwa da yawa”

“Zan yi murna domin a yanzu haka, alabashi na bay a isa na. Hakan ya s ana bar mota a gida domin bazan iya sayab mai in zo aiki da shi ba. Saboda da haka motar kasuwa ko bas na ke shiga. Idan zan iya samun dubu 200 ko sama da shi akan albashi na, zan iya sayan mai a mota in zo aiki” a ccewar wani ma’aikacin gwamnati, Shedrack Titus.

Yayin da gwamnati ta kaddamar da kwamitin nazarin sabon albashi mafi karanci, abin jira a gani shi ne tabbatuwar al’amarin. A shekarun baya, an yi ta kai ruwa rana tsakanin gwamati da kungiyoyin kwadigo a game da karin albashin ma’aikata – kuma ko da aka amince da naira dubu talatin a matsayin albashi mafi karanci a 2019, har yanzu akwai gwamnatoci da dama da ma’aikatu da ba su kaddamar da albashin na dubu talatin ba.

Alkaluman Hukumar Kididdiga ta Kasa sun nuna a halin yanzu, hauhawar farashin kaya a kasar ya kai kashi 28 cikin dari – lamarin da ya sa farashin akasarin kaya a kasuwanni ya rubanya sau fiye da uku a cikin shekaru hudu da suka gabata.

A 2019 lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriyar ta amince ta biya sabon tsarin albashi mafi karanci na naira dubu talatin daga naira dubu 18, hauhawar farashin kaya ya na mataki na kashi 11 cikin dari ne.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG