Tinubu Ya Ba Da Umarnin Farfado Da Na’urar Bin Diddigin Ayyukan Gwamnati

Shugaba Tinubu (Hoto: Fadar Shugaban Najeriya)

Tsarin dai na da nufin bai wa 'yan Najeriya damar sanya ido kan yadda ake gudanar da ayyuka daban-daban a fadin kasar nan take.

A wani yunkuri na inganta ayyukan ‘yan kasa a harkar mulki, Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarni na farfado da na’urar bin diddign ayyukan gwamnati.

Tsarin dai na da nufin bai wa 'yan Najeriya damar sanya ido kan yadda ake gudanar da ayyuka daban-daban a fadin kasar nan take.

Da yake jawabi a karshen taron kwanaki uku na Majalisar zartarwa da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a, Shugaba Tinubu ya jaddada kudirinsa na ganin an samar da tsarin gudanar da mulki cikin gaskiya da rikon amana, inda ya jaddada muhimmancin baiwa ‘yan kasa damar sanya ido kan yadda ake gudanar da ayyuka a fadin kasar.

Domin tabbatar da ingantaccen tsarin bin diddigin, Shugaba Tinubu ya damka ragamar aikin wa mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin siyasa da tsare-tsare, Hadiza Bala Usman, domin farfado da tsarin ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Da yake jawabi, Tinubu ya bukaci mambobin majalisar ministocinsa da su kara himma wajen biyan bukatun al'ummar Najeriya.