Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Kasafin Kudin Naira Tiriliyan 2.17 Da Shugaba Tinubu Ya Mika Wa Majalisa Ya Haifar Da Cece-kuce


Shubaga Bola Tinubu a tsaye yana magana (Hoto: Facebook/Tinubu)
Shubaga Bola Tinubu a tsaye yana magana (Hoto: Facebook/Tinubu)

'Yan Najeriya sun yi tir da Allah wadai da karin kasafin kudin da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya turawa Majalisa inda ya bayyana bukatar kudin domin sayen jirgin ruwa na kawa da kuma ware wani kaso da nufin bunkasa wani tsarin Ilimi.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika wa Majalisar Dokoki karin kasafin kudi Naira tiriliyan 2.17, wanda ya hada da shirin ware naira biliyan 5 don sayen jirgin ruwa na Shugaban kasa, da naira biliyan 5.5 na asusun ba da lamuni na ilimi.

Sannan kuma za a sayi motoci na alfarma domin uwargidan Shugaban kasa wanda za su ci kimanin naira biliyan daya da rabi.

Sai dai ‘Yan Najeriya sun bayyana bacin ransu a shafukan sada zumunta kan matakin da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ta dauka na karin kasafin kudin cikon gibin. Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Tinubu ke ci gaba da karfafa gwiwar ‘yan Najeriya da su yi sadaukarwa a cikin halin da ake ciki na matsin tattalin arziki sakamakon janye tallafin man fetur.

Karin kasafin kudin dai ya hada da Naira biliyan 4 domin gyara gidajen Shugaban kasa da kuma Naira biliyan 2.5 na gidan mataimakin Shugaban kasa. Haka kuma, gwamnati na shirin kashe Naira biliyan 2.9 wajen sayen motoci kirar (SUVs) na fadar Shugaban kasa da kuma karin Naira biliyan 2.9 don maye gurbin motocin da za su yi aiki a fadar shugaban kasa, sa’annan an ware karin Naira biliyan 1.5 na motoci ga ofishin uwargidan shugaban kasa.

Uwargidan Shugaba Tinubu, Oluremi Tinubu
Uwargidan Shugaba Tinubu, Oluremi Tinubu

A cikin karin kasafin kudin, rundunar sojin ruwan Najeriya ta gabatar da kudirin kudi kimanin biliyan 42.3 da kuma kashe naira biliyan 20.42 wanda jimillan su ya kai kimanin kasafin kusan naira biliyan 62.8.

Sauran abubuwan da ke cikin kudirin kasafin kudin daga rundunar sojojin ruwan Najeriya sun hada da sayen motoci, gina sansanin sojin ruwa a Lekki da Epe, da samar da muhimman kayan aiki, da kuma sayan alburusai.

Karin kasafin kudin cikon gibin da gwamnatin Shugaba Tinubu tayi, ya haifar da muhawara tare da cece-kuce musamman a shafukan sada zumunta da kafafen labarai na kasa inda ‘yan Najeriya da dama ke ganin bai kamata gwamnati ta kashe irin wadannan makudan kudade duk da lura da halin da talakawa ke ciki a kasar na matsin tattalin arziki, bayan kira da gwamnatin ta rinka yi na cewa talaka ya jure domin akwai dadi a gaba.

Manhajar X
Manhajar X

A manhajar X da muhawar tafi zafi da daukar hankali,Eyenidara Essien ya ce;

“Shugaba Tinubu wanda ke shirin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 15 daga kangin talauci wajen raba kudaden jinkai wata na naire dubu 25, zai zauna a cikin jirgin ruwa na biliyan 5. ga matarsa Fasto mai wa’azi ba za ta tunatar da shi labarin attajiri Lazarus da aka anbato shi a Littafi Mai Tsarki ”.

Shima Prexxy mai dauke da linzami mai suna @prehfred na manhajar X cewa yayi,“Matsalolin Najeriya sun yi yawa ga duk wanda ya mamaye ofishin shugaban kasa ya yi tunanin hutu. Kamata ya yi ya shagaltu da magance matsalolin da suka addabi al’ummar kasar nan, ba sayen manyan motoci, jirgin sama ko jirgin ruwa na alfarma ba…..”

Sannan shima M.S Muhammad ya ce “Abinda bana goyon baya daya shine batun sayan jirgin ruwa, amma banda wannan bani da matsala, domin tafiyar da gwamnatin tarayya akwai tsada”

Dangane da batun aiwatar da dokar manyan makarantu da shugaba Tinubu ya sanya wa hannu a watan Yuni, gwamnati ta sanar da cewa an dage aiwatar da dokar da aka shirya gudanarwa tun a watan Satumba zuwa watan Janairun 2024.

Shugaba Bola Tinubu ne da kanshi ya jaddada haka yayin wani jawabi na baya-bayan nan a taron Majalisar tattalin arzikin kasa, inda yace "dole ne a fara shi a watan Janairu 2024" bayan jinkirin farko.

Asusun ba da lamuni na ilimi wanda dokar ta samar kuma babban bankin Najeriya (CBN) ne ke kula da shi, Dokar ta zayyana hanyoyin samar da kudade da suka hada da kashi daya cikin 100 na duk ribar da gwamnatin tarayya ke samu daga man fetur da sauran ma’adanai; kashi daya cikin 100 na haraji, da haraji da ake samu ga gwamnatin tarayya daga Hukumar Harajin ta Tarayya (FIRS), Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) da Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS); tsare-tsaren tallafin ilimi da tallafin ilimi. Har ila yau, za a ba da rancen kuɗi ta hanyar gudummawa, kyauta, tallafi da sauransu.

Biyan bashin kudin tallafin ilimin an tsara shi yadda zai fara ne daidai shekaru biyu bayan kammala shiga cikin shirin yiwa kasa hidima na NYSC, kamar yadda dokar ta tanada.

Tun daga farkonsa, kudirin, wanda yanzu ya zama doka, ya haifar da cece-kuce inda wasu sassan jama'a ke zargin gwamnati da yunkurin wanke hannunta daga kudaden tallafin manyan makarantu. Wanda rashin isassun kudi a cibiyoyin na ilimi na daga cikin manyan dalilan da ya sanya suke tafiya yajin aiki kamar ruwan dare, lamarin da ya haddabi gwamnati da ‘yan kasa musamman dalibai na ilimi.

Yanzu dai ‘yan Najeriya na cigaba da sanya ido zuwa ranar da zasu sami saukin rayuwa da tabbataccen rage radadin da suke ciki musamman a sakamakon cire tallafin mai da ya haifar da hauhawan farashin kaya da matsin tattalin arziki a Najeriya.

~ Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG