Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Jamus Olaf Scholz Ya Nuna Sha’awar Kulla Alakar Kasuwanci Da Najeriya


Nigeria-Germany - Kasuwanci
Nigeria-Germany - Kasuwanci

Yayin da Shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Olaf Scholz da tawagarsa suka kai ziyarar aiki Najeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a jawabinsa ya jaddada kudirin gwamnatinsa na sauya Najeriya daga kasa mai rarrafe izuwa kasa mai dimbin ci gaba.

ABUJA, NIGERIA - Hakan na da nufin samar da sauye-sauye masu inganci ta hanyar gudanar da shugabanci mai inganci.

Jawabin nasa ya fito ne a tattaunawar da suka yi da shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Olaf Scholz, da tawagarsa a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Lahadi.

A yayin ganawar, shugaba Tinubu ya bukaci inganta hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Jamus a bangarori daban-daban da suka hada da tsaro, albarkatun kasa, ilimi, da tsarin dimokuradiyya.

Shugaba Tinubu ya jaddada nasarar da ya samu na shari’ar da kotun koli ta yanke a baya-bayan nan na tabbatar da nasararsa a matsayin wani al’amari da ya kawar masa da duk wani abu da ya dame shi, kuma hakan zai ba shi dama ya maida hankali wajen aikin kawo wa kasa cigaba ba tare da wata tantama ba.

Shugaba Tinubu ya ci gaba da nuna kyakkyawar maraba ga gwamnatin Jamus don kara hadin gwiwa a bangarori da dama kuma ya bayyana aniyarsa ta sa Najeriya ta samu ci gaba mai inganci, inda ya amince cewa har yanzu kasar na fuskantar manyan kalubale.

A jawabinsa, shugaban gwamnatin Jamus, Chancellor Scholz ya jaddada muhimmancin kara kokarin hadin gwiwa, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, tare da mayar da hankali kan wutar lantarki da makamashi.

Da yake nuna godiya ga gudummawar da Shugaba Tinubu ya bayar ga kungiyar ECOWAS, Chancellor Scholz ya kuma jaddada bukatar daukar matakan hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka da ma duniya baki daya.

A tattaunawarsa da manema labarai, Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya nuna kudiri da sha’awar kulla alaka da Najeriya na kasuwanci musamman a bangaren iskar gas daga Najeriya, musamman wajen yinkuri na cike gurbin kasar Rasha.

-Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG