A jawabin bude wani taro na kwanaki uku, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamnatinsa ta yi nasara wajen cimma burin ‘yan Najeriya da suka zabe shi.
Taron da aka fara ranar Laraba, an shirya shi ne don ministoci, hadiman shugaban kasa, da manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnati, da kuma manyan jami’an gwamnati a fadar gwamnati da ke Abuja.
Shugaban ya bukaci ministocinsa, masu ba shi shawara da sauran jami’an gwamnati da su taimaka masa wajen cimma wannan burin, inda ya jaddada cewa ya zabe su ne don su taimake shi ya yi nasara.”
“Duk wanda ke aiki yadda ya kamata, ba shi da wata matsala, idan ba ka aiki yadda ya kamata, zamu duba mu gani. Idan kuma ba za ka iya ba, to sai ka bar mu," a cewar shugaban.
Tinubu ya kuma bayyana cewa kowanne dan Adam ajizi ne, shi ma zai iya yin kuskure, amma idan aka nuna masa kuskuren da ya yi, to zai gyara. Ya kuma bayyana cewa shi shugaban dukkan ‘yan Najeriya ne ba tare da la'akari da bambancin jam’iyya ba.
Dandalin Mu Tattauna