Tina Turner, ta rasu tana da shekara 83

Obit Tina Turner

Turner ta rasu ranar Talata, bayan doguwar jinya a gidanta dake Küsnacht kusa da Zurich, a cewar manajanta. Ta zama 'yar kasar Switzerland ne shekaru goma da suka wuce.

WASHINGTON, D.C.- Tina Turner, fitacciyar tauraruwar da ta yi shahararriyar wakar "What’s Love Gotta Do With It," ta rasu tana da shekara 83.

An haife ta da sunan Anna Mae Bullock a wani kebabben asibitin na Tennessee dake Amurka, daga baya ta auri Ike Turner ya canza mata suna zuwa Tina ta kuma dauki sunan shi na Turner, ta kasance Tina Turner.

Obit Tina Turner

Ta wahala sosai cikin auren ta, inda Ike yakan yi mata duka ta yi ta fama da rauni a jiki, ta kan shiga cikin rudani don azaba, ga kuma rashin kudi a cikin shekaru 20 da tayi tana dangantaka da Ike Turner, amma ta zama tauraruwa da kanta bayan da ta cika shekaru 40, a lokacin da tauraron yawancin takwarorinta ke dushewa, kuma ta kasance babbar mai kide kide bayan shekaru har ya zuwa rasuwarta.

FILES-ENTERTAINMENT-MUSIC-US-SWITZERLAND

Sun yi yawo kasashe akai-akai na tsawon shekaru, suna maka, a wani bangare saboda Ike sau da yawa yana da yawan samun karancin kudi dole suka yi ta yawo suna waka. Ya kuma tilastawa Tina ta yi rawa da waka bayan ya yi mata duka har a lokacin da take da ciwon sankara, da ciwon huhu, tare da rugujewar huhu, wataran ta taba yin waka da jini cike a bakinta bayan yayi mata duka, ya fasa mata kashin baki. Ya kan yi mata duka ya watsa mata shayi mai zafi a fuska, sannan ya yi mata fyade.

"Tina – The Tina Turner Musical" Broadway Opening Night

Amma bayan shekaru da dama da Ike wataran ya na barci a hotel din da suka sauka, sai ta sace jiki cikin dare daga ita sai wani katin tafiya da kwabo 36 a aljihunta ta tsere.

Ta hanyar jajircewarta wajen ba da labarinta, yunkurin da ta yi na ci gaba da kasancewa a cikin rayuwarta, ko da sadaukarwarta, ta baiwa mata dayawa kwarin guiwa, wajen zama daya daga cikin mata na farko da suka bayyana wahalarsu cikin aure.

Obit Tina Turner

Tina Turner ta nuna wa wasu, wadanda suke rayuwa cikin tsoro yadda kyakkyawar makoma mai cike da soyayya, tausayi, da yanci yakamata su kasance.

Manyan shahararrun mawaka sun bayyana irin taimako da tayi musu lokacin tasowarsu, kuma sun nuna bakin cikin su da rasuwarta.