Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Da Taimakon Wani Na Samu Daukaka Ba – Burna Boy


Burna Boy (Hoto: Instagram)
Burna Boy (Hoto: Instagram)

Ga dukkan alamu, kurar da ta tashi bayan bikin karrama mawaka na Grammy da aka yi a Amurka a makon da ya gabata, ba ta kwanta ba, domin har yanzu ana ci gaba da ka-ce-na-ce musamman a Najeriya da aka karrama mawakanta biyu.

Ko da yake, ga wadanda suka saba bibiyar wannan biki a duk shekara, wannan ba bakon abu ba ne musamman a Amurka – amma a wannan karon ma Najeriya ma ta dauki dumi.

Tun bayan da mawakan Najeriya biyu, Burna Boy da Wizkid da suka shahara a salon wakokin Afrobeats suka samu nasarar lashe wannan lambar yabo, ake ta gutsiri-tsoma, kama daga mawakan zuwa masoyansu.

Davido, (hagu) Burna Boy (tsakiya) Wizkid (dama) (Hoto: Shafukansu na Instagram)
Davido, (hagu) Burna Boy (tsakiya) Wizkid (dama) (Hoto: Shafukansu na Instagram)

Mafi akasarin muhawarar da ta barke a Najeriya, ana yin ta ne kan wanda ya cancanta da wanda bai cancanta ba, musamma yadda masoyan Davido suke ganin an ci bikin babu su.

Ba a Najeriya kadai ba, a Ghana ma da ke makwabtaka da ita, masoya wakokin Afrobeats a kasar sun yi ca akan mawakan Ghanar, inda suka rika musu gori kan yadda suna kallo takwarorinsu na Najeriya suka daga tuta a bikin na Grammy.

Masu korafin a Ghana, sun kuma yi nuni da yadda mawakansu suka tsaya a sayen maka-makan gidaje, kalaman da ba su yi wa shahararren mawakin kasar Shatta Wale dadi ba.

“Ni lambar yabota ta Grammy ita ce ta kadarorin gidaje.” Shatta Wale ya ce.

Shatta Wale, mawakin Ghana (Hoto: Manuel Instagram)
Shatta Wale, mawakin Ghana (Hoto: Manuel Instagram)

Jim kadan bayan kammala bikin na Grammy, matashin mawaki Rema, wanda shi ma dan Najeriya ne, ya fito ya yi zargin cewa ana danne irin nasarorin da ya samu, “saboda an ganni matashi ne.” In ji Rema.

Rema (Hoto: Shafin Instagram)
Rema (Hoto: Shafin Instagram)

Ko da yake, Rema bai fito ya yi nuni da bikin na Grammy ba, amma lura da cewa kalaman nasa na zuwa ne kwanakin kadan bayan bikin, ya sa mutane da dama suke ganin yana korafi ne kan yadda aka ba da lambaobin yabo a bikin na Grammy ba tare da shi.

A shekarar 2019, tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya lissafa wakar Rema ta “Iron Man” a cikin wakokin da ya fi saurare.

Shi dai Davido da ake kallon suna hammaya da Burna Boy da Wizkid, ya fito jim kadan bayan karrama su da lambobin yabon, ya taya su murna.

“Ko ta wacce fuska ka kalli wannan (lambar yabo,) babbar nasara ce ga Najeriya, al’adunta, da al’umarta! Ina taya dukkan wadanda suka samu wannan kyauta murna!" In Ji Davido.

Kwatsam ana kan wannan ka-ce-na-ce, a ranar Asabar, Burna Boy ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter da yake da mabiya miliyan 5.1, wanda wasu da dama suka fassara a matsayin magana ce ta gugar zana, lamarin da ya sa har masoyan Wizkid wanda abokinsa ne, suka ga kamar kalaman sun yi cin fuska.

Shi dai Burna Boy ya wallafa wasu kalamai da ke nuni da cewa, ba da taimakon kowa ya samu nasarar lashe wannan lambar yabo ba.

“’Ya’yana za su bugi kirji su ce, “Baba da kansa ya samu daukaka, mu ma za mu iya mu kadai.”

Wadannan kalamai ba su yi wa wasu masoyan Wizkid dadi ba, saboda shi (Wizkid) ya samu lambar yabonsa ta Grammy ne karkashin wakar Beyonce “Brown Skin Girl,” yayin da shi kuma Burna Boy ya samu ne karkashin kundin wakokinsa na kashin kansa wato “Twice as Tall.”

Abin nufi anan shi ne, shi Wizkid Beyonce ta rike hannunsa ya samu lambar yabon yayin da shi Burna da aikin da ya yi da kansa aka karrama shi.

Ko da yake wasu na ganin ba hakan yake nufi, magana ce kawai ya yi ta a zube ba tare da yana nufin wani abu ba.

Mawakin wanda dan asalin birnin Fatakwal ne, ya samu lambar yabo ta mawakin da kundin wakokinsa ya fi fice a duniya.

Tuni dai shafukan sada zumunta na Twitter da Instagram suka bige da ce-ce-ku-ce, inda yayin da wasu ke sukar kalaman nasa wasu kuwa yabonsa suke yi.

Ga dukkan alamu, ko da wannan batu na Grammy ya shude, akwai alamu da ke nuna cewa ya bude a wani sabon babi da zai kara rura wutar hamayyar da ke tsakanin mawakan Najeriya da masoyansu.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG