Ban da na Adamawa inda manyan 'yan siyasar jihar suka yiwa Nuhu Ribadu muba'aya na Yobe da aka sanar cewa tsohon minista Adamu Maina Waziri shi ya lashe zaben ya sanya sauran 'yan takarar kin amincewa da sakamakon.
Amma Adamu Maina Waziri yace dama haka gasar siyasa ta gada. Yace dimokradiya tana da ma'auni. Ma'aunin kuwa shi ne za'a yi zabe wani zai ci wani zai fadi. Yace suna da wakilai 21 a cikinsu 19 sun zabeshi biyu kuma sun zabi Dr Ingama wanda yana cikin wadanda suka kauracewa zaben.
Tsohon ministan ma'aikatar kudi Dr Yerima Lawal Ingama yace indai har ba'a gyara zaben ba tamkar PDP ta fadi a jihar Yobe ke nan. Dr Ingama yace shirme ma ya fi zaben. Ba maganar rashin adalci ba ne kawai. Shirita ce kawai. Basu yi tsammanin shugabanninsu na PDP zasu amince da shirmen da aka yi ba.
A cikin mutum hudu da suka fito takara uku basu san ma an yi zaben ba. Kawai dai Alhaji Adamu Maina ya tara mukarrabansa yayi zabe shi kadai kuma yace shi ya ci. Yace ko mahaukaci yana nada kansa sarki. Yace shi ke nan Yoben tana nan sai ya je yayi takama a kai. Basu yadda jam'yyar PDP zata karbeshi ba.
Masu zaben dari shida da saba'in ne. Maina Waziri ya kwakulo mutum ashirin da daya suka je su zabeshi. Sauran su uku ma basu san an yi zabe ba.
Bisa abun dake faruwa Ibrahim Talba da Hassan Kafayo dake marawa Ingama baya sun ce lallai PDP tayi hatara.
Adamu Maina dai yace 'yan takarar tamkar sun yi masa taron dangi ne. Sun mayar dashi saniyar ware domin suna gani shi ne yake da nasara. Injishi duk manyan garuruwan Yobe suna murna jan gwarzo zai zo ya zama gwamnansu.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5