Manyan 'yan jam'iyyar PDP sun ce an tursasawa masu kada kuri'a ne domin su zabi dan takarar da gwamna ke marawa baya sabili da haka ba zasu amince da sakamakon zaben ba.
Muhammad Ali Pate daya daga cikin wadanda suka tsaya takarar yace a ganinsu akwai rashin adalci a cikin zaben. Yanzu suna binciken zargin cewa an tilastawa wakilan zaben. Ali Pate yayi zargin cewa an tilastawa masu zabe kana wasu cikinsu an tsoratasu. An tsorata masu zabe cewa idan basu zabi dan takarar da gwamna ke marawa baya ba zasu dandana kudarsu.
A jihar Gombe kuwa duk zabubukan fidda gwani a jam'iyyun PDP da APC tubarkalla. An gudanar dasu ba tare da wata tangarda ba.
Jam'iyyar PDP ta sake tsayar da Gwamna Hassan Dankwambo a matsayin gwaninta. Yayi jawabi na godiya ga Allah da irin hadin kan da aka samu da yadda suka amince dashi. Yace da yaddar Allah zai cigaba da yin mulki nagari ba tare da kutuntawa kowa ba amma na cigaban jama'a da jihar.
Inuwa Yahaya shi ya zama dan takarar jam'iyyar APC. Yace yaji dadi da nasarar da ya samu.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.