Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kusoshin PDP a Jihar Adamawa Zasu Kauracewa Babban Taron PDP


PDP
PDP

Wasu kusoshin PDP sun nuna fushinsu game da zaben fidda gwani da aka gudanar a Abuja maimakon cikin jihar.

A zaben da aka ce an yi a Abuja Malam Nuhu Ribadu tsohon shugaban EFCC aka ce ya lashe zaben.

To amma zaben ya bar baya da kura. A taron manema labarai da kusoshin jam'iyyar suka kira da ya kunshi Chief Joel Hamanjore Madaki da uwar jam'iyyar ta kasa ta dakatar da sakataren jam'iyyar Barister A.T.Shehu da shi ma aka dakatar da wasu 'yan takarar jam'iyyar sun sha alwashin kauracewa babban taron da za'a yi a Abuja yau.

Wasu 'yan takarar kujerar gwamnan Dr Ahmad Modibo da Injiniya Marcus Gundiri sun ce wadanda suka gudanar da zaben a Abuja 'yan ta'ada ne wadanda basa bin dokokin kasa ko na jam'iyya. Wai su ne zasu san yadda zasu bayyanawa mutanen Adamawa akan abun da ya faru a Abuja.

Kodayake gwamnan jihar Barrister Bala John Ngilari bai halarci taron ba amma ya aika da daraktan kemfen dinsa tsohon dan majalisar dattawa Sanata Abubakar Gire. Yace a wannan karon Adamawa ba zata yadda a yi mata nadi ba.

A jihar Taraba ma maganar daya ce. Mukaddashin gwamnan jihar Sani Abubakar Danladi ya garzaya zuwa Abuja inda yake bukatar a sake wakilan da zasu yi zaben fidda gwani domin a cewarsa duk wakilan tsohon mukaddashin gwamna ne wato Garba Umar UTC. Amma Injiniya Yusuf Gamalia na bangaren Umaru Garba yace su sun shirya zasu shiga zaben fidda dan takarar kujerar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG