A wasu wuraren ma rigingimun sai da suka kaiga ba hammata iska.
A jihar Sokoto 'yan takara hudu ne suka fafata. Sun hada da mataimakin gwamnan jihar Barrister Mukhtari Shagari, Sanata Abdalla Wali, Sanata Abubakar Umar Gada da kuma tsohon ministan wasanni Yusuf Suleiman. Amma Suleiman ya kauracewa zaben ana sauran kwana daya a gudanar dashi bisa zargin cewa za'a shirya coge.
Bayan an yi wuni guda ana tantance 'yan takara kuma gap da ake shirin soma zaben da misalin karfe goma sha daya na daren Litinin sai Barrister Shagari yayi kokarin dakatar da zaben bisa zargin shirin tafka magudi. Yace kamata yayi an gama zaben sa'o'i hudu da suka wuce. Wakilan ainihi basu da yawa sai aka kawo wasu aka cika wurin dasu. Sabili da haka yace a matsayinsa na shugaban jam'iyyar na jiha ya kira shugaban jam'iyyar na kasa Adamu Mu'azu ya soke kwamitin da aka turo domin a turo wadanda zasu yi zaben bisa gaskiya.
Daga bisani mataimakin gwamnan ya kauracewa zaben amma an cigaba tsakanin 'yan takara biyu da suka rage inda Sanata Abdalla Wali ya zama dan takarar PDP na kujerar gwamnan Sokoto.
A jihar Kebbi 'yan takara 13 suka fafata domin fidda gwani na gwamna a jam'iyyar PDP. Amma rigingimu da korafe korafe sun sa an dakatar da zaben. Wadanda suka yi zargin sun hada da mataimakin gwamnan jihar da Sanata Muhammad Magoro da tsohon minista Samaila Sambawa. Sun zargi gwamnatin jihar da fifita wani dan takara.
Amma abun mamaki an bada sanarwa a kafofin yada labarai cewa Janaral Bello Sarkin Yaki wanda suka ce shi ne gwamnan jihar ke marawa baya, ya ci zaben. Haka ya sa 'yan takarar takwas sun shirya taron 'yan jarida inda suka nuna rashin amincewarsu.
A jihar Zamfara an kwashe ranaku biyu ana gudanar da zaben amma har yanzu ba'a fitarda gwani ba. Daga karshe dai an dunguma zuwa Abuja domin warware bakin zaren.
Ga cikakken rahoton Murta Umar Sanyinna.