Shugaban kwamitin shirya zaben da PDP ta tura zuwa jihar Neja Sanata Martins Kuye yace Alhaji Nasko ya lashe zaben da kuri'u 908.
Wanda ya zo na biyu shi ne Injiniya Hannafi Sudan da kuri'u hamsin da bakwai. Mataimakin gwamnan na yanzu Alhaji Ahmed Musa Ibeto ya samu kuri'u talatin da hudu. Sauran 'yan takarar duk sun samu kuri'u goma sha daya daya ne. Amma a ranar shirya zaben Sanata Nuhu Aliyu ya bayyana janyewa daga takarar domin yace ya gano babu shirin yin adalci a zaben.
Duk 'yan takarar sun kira taron manema labarai inda suka bayyana matsayinsu. Injiniya Mustapha Bello shi yayi magana a madadin wadanda suka fadi. Ya bayyana dalilinsu na daukan matakin. Yace gwamna shi ya nunawa mutane yadda zasu yi zabe sabanin yadda yakamata a yi. Gwamnan ya baiwa daya daga cikin masu goyon bayan dan takararsa ya cika masa. Daga nan ya kada tashi kuri'ar. Daga yin hakan duk wanda ya biyo bayansa abun da yayi ke nan.
Shi ma mataimakin gwamnan jihar Alhaji Ahmed Musa Ibeto ya jaddada matsayinsu na yin fatali da sakamakon zaben. Wakilan 'yan takarar basu sanya hannu a sakamakon zaben ba.
Daya daga cikin wakilan Alhaji Nasko yace mika kuri'ar da gwamnan yayi domin a rubuta sunansa bai sabawa ka'ida ba. Wai gwamnan yayi hakan ne ya nunawa duniya cewa shi ba munafiki ba ne.
To saidai Alhaji Umar Nasko ya nemi hadin kan sauran 'yan takarar. Ya rokesu da sunan Allah da annabinsa su hada hannu domin su shiga yaki da karfi.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.