Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, na karbar bakuncin shugabannin manyan kasashen duniya da suka fi karfin tattalin arziki wadanda ake wa lakabi da G20.
Taron zai yi dubi ne kan yadda za a warware matsaloloin da suka sha musu kai, kamar na hadahadar kasuwancin da yaki da ta'addanci da sauyin yanayi.
Ko da yake har yanzu babu wata matsaya kan batutuwan da suka shafi sauyin yanayi da kuma cinikayya.
Babu daidaito tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da sauran shugabannin manyan kasashen duniya, tun lokacin da ya cire Amurka daga yarjejeniyar da aka kulla a Paris don tukarar sauyin yanayi.
Trump ya ce yana shirin kakaba haraji ga duk karafunan da za a shigo da su Amurka, wanda hakan ke zama wata babbar barazana wajen kare kamfanonin Amurka, wanda hakan ya ta da hankalin shugabannin na G20.