Shugaban Amurka Donald Trump ya ziyarci birnin Warsaw dake kasar Poland inda ya gabatar da jawabi ga shugabannin da kuma dumbin jama'ar kasar da suka halarci wajen jawabin.
A lokacin jawabin shugaba Donald Trump y ayi gargadin cewa akwai babbar barazana ga tsaro da kuma rayuka, ya kuma ce iyakokin Amurka za su ci gaba da zama a rufe ga masu ayyukan ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi.
Trump ya ce Amurka ba za ta amince da masu kyamar al’adunta ba, suna fake wa da kiyayya a matsayin dalilin da ya sa suke tayarwa da bayin Allah hankali.
Haka kuma a yau ne, shugaban na Amurka, ya yi kira ga kasashen duniya akan su tunkari barazanar da Korea ta arewa ke yi, su kuma fito fili su nuna wa kasar cewa akwai mummunan sakamakon idan ta ci gaba da wannan mummunar dabi'ar ta ta.
Trump ya ce ba shi ne zai yi wa Korea ta Arewa iyaka ba ko ya bayyana shirin da yake yi a kanta, amma yana da tsauraran matakan da ya ke tunani.
Sai dai bai fito fili ya fadi matakan da yake so ya dauka ba.
A jiya Laraba jakadiyar Amurka a Majalissa Dinkin Duniya Nikki Haley ta fadawa Kwamitin Sulhun na Majalissar cewa Amurka na shirye ta yi amfani da karfin soja wajen magance barazanar da Korea ta Arewa ta yi, na harba makami mai linzami.
Amma ta ce zai fi dace wa a warware rikicin ta hanyar diplomasiyya da kuma daukar matakan kakaba takunkumin tattalin arzikin akan kasar.
Facebook Forum