Qatar ta bada sanarwar shirinta na kara samar da iskar gas, mataki da ake ganin ta dauka ne domin shirye shiryen tsawaita takaddamar tsakaninta da wasu makwabtanta na yankin Gulf.
Hukumar samar da man fetir ta gwamnatin Qatar ta fada a jiya Talata cewar zata inganta samar da iskar gas na amfanin cikin gida da kashi 30 cikin dari, cikin yan shekaru masu zuwa.
Za a gudanar da Karin ne a yankin arewacin kasar, inda ake da tarin iskar gas fiye da ko ina a duniya, wanda Qatar da Iran suke ginawa.
Wannan sanarwar ta jiya Talata a kan makamashi, Qatar ta bayar ne a yayinda wa’adin da Saudia da Hadaddiyar daular kasashen Larabawa da Masar suka gindaya mata game da jerin bukatu ke lebe. Matakin da ya kai ga manyan kasashen uku suka yanke huldan diplomasiya da ta kasuwanci da Qatar wata guda da ya wuce.
Facebook Forum