Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump Ya Fara Rangadin Diplomasiya na Farko


Shugaba Donald Trump da maidakinsa Melania Trump sun isa Warsaw, Poland, July 5, 2017.
Shugaba Donald Trump da maidakinsa Melania Trump sun isa Warsaw, Poland, July 5, 2017.

Shugaba Donald Trump ya fara ran gadinsa na farko , na tsawon kwanaki 4 akan abinda ya shafi harkokin diflomasiyya a kasashen yammacin Turai, wanda yanzu haka ya sauka fadar gwamnatin kasar Poland tun da yammacin jiya laraba.

Yayinda shugaban ke fatar samun kyakkyawar marhabin, haka kuma zai fuskanci damuwa a nahiyar sakamakon wasu kalaman manufofin gwamnatinsa da ya furta farko-farkon kama mulki.

Wadansu daga cikin wadannan batutuwa ko sun hada da batun NATO, shawarar da yace yana son ya dauka game da ficewar Amurka daga kungiyar nan ta Faris dangane da batun canjin yanayi, sai kuma batun kalaman sa game da shugaban kasar Russia Vladimir Puttin.

Trump dai zai gabatar da jawabin sa na farko ne a nahiyar, bayan wanda zai gabatar a yau alhamis a dandalin Krasinski dake Warsar, Wurin da yake da yawan alamomin nuna kin jinin mulki danniya da kama karya.

Sojojin Amirka sama da dubu 3 ne aka girke a Poland din a matsayin wani bangare na NATO, wanda aka samar da niyyar mayar da martini ga kasar Rasha sabili da rawar take takawa a kasar Ukraine.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG