Da take jawabi jiya a wajen taron kasuwanci da zuba jarin Afrika da aka gudanar a cibiyar taron Eko dake jihar Legas, mai baiwa Amurka shawara kan harkokin kasuwanci Julie LeBlanc, ta ce a shekarar da ta gabata kadai, Amurka ta tallafa tare da kammala wasu sabbin yarjejeniyoyin guda 547, wadanda suka kai kimanin dala biliyan 14.2, wanda ke nuna karuwar kashi 60 cikin 100 na adadin da kuma darajar yarjejeniyoyi da aka cimma idan aka kwatanta da shekarar 2022.
LeBlanc ta ce, ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai kasashem yammacin Afirka ciki har da Najeriya, Cape Verde, Cote d'Ivoire, da Angola, ya nuna aniyar kudurin da Amurka ta dauka kan Afirka kwanan nan.
“Wannan ziyarar ta karfafa himmarmu wajen inganta hadin gwiwar tsaro, ayyukan kiwon lafiya, da bunkasar tattalin arziki a yankin."
“Gudunmawar da gwamnatin Amurka ta bayar na dala miliyan 160 don tallafawa cinikayya a Nahiyar Afirka ya misalta kudurinmu. Manufarmu wannan tallafin, ita ce faɗaɗa cinikayya da kuma tallafawa Mata da Matasa a Nahiyar Afirka."
LeBlanc ta cigaba da cewa: “Najeriya tana daya daga cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a Nahiyar, mun fahimci muhimmiyar rawar da take takawa a kasuwannin yanki da na duniya. Najeriya ta kasance babbar abokiyar cinikayyarmu ta biyu a Afirka."
“Muna ganin Nijeriya a matsayin babbar shugaba a Nahiyar, kuma babbar abokiyar tarayya wajen ciyar da kyawawan dabi’unmu. Abin da ya amfanar da Nijeriya, zai amfanar da Afirka, da ma duniya baki daya.”