Taron Kolin MDD: Shugabannin Kasashe Zasu Kaddamar Da Tattaunawa Kan Tsaron Duniya

78th UNGA General Debate at UN HQ in New York

A yau Talata shugabannin kasashen duniya zasu kaddamar da taron da suke yi a duk shekara a babban zauren MDD a karkashin maudu’an da suka hada da karuwar rabuwar hannu tsakanin al’ummar duniya da manyan yake-yaken dake gudana a Gaza da Ukraine, Sudan da kuma barazar yakin yankin Gabas ta Tsakiya

A jawabinsa na sharar fage akan “halin da duniya ke ciki” da ya gabatar ga shugabannin kasashe da sarakuna da ministoci a ranar Lahadi mai taken “taron koli kan makomar duniya”, Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yace, duniyarmu ta saki hanya-kuma akwai bukatar daukar tsauraran matakai domin dawo da ita kan tafarki.”

Ya yi tsokaci akan rikice-rikicen dake “kara zafafawa suna hayayyafa, daga gabas ta tsakiya zuwa kasashen Ukraine da Sudan, kuma babu wanda ya san ranar kawo karshensu” sannan yayi batu akan tsarin samarda tsaro a duniya, wanda ya ce yana fuskantar barazanar rabuwar hannu daga kasashen duniya da yaduwar makaman nukiliya dana wanzuwar sabbin makamai da fagagen daga.”

UNGA

Haka kuma ya yi karin haske akan matsalar rashin daidaito da rashin tsarin kasashen duniya na fuskantar barazanar dake kunno kai ko wacce ake da ita, da kuma mummunan tasirin sauyin yanayi.

-AP