Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UNGA: An Bude Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya A Birnin New York


United Nations General Assembly
United Nations General Assembly

Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya hado kan shugabannin kasashen duniya a birnin New York a wannan mako, inda tarukan da za a gudanar a ranar bude taron, za su mai da hankali kan kara kaimi wajen cimma muradun samar da ci gaba a duniya.

WASHINGTON, D.C. - Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa kashi 15 cikin 100 na muradun ci gaba, a ciki 17 ne ke kan hanyar da za a iya cimmawa nan da shekarar 2030.

U - Antonio Guterres
U - Antonio Guterres

"Taron kolin samar da ci gaban karni zai kasance lokacin da gwamnatoci za su zauna a teburin da tsare-tsare da shawarwari don hanzarta ci gaba," in ji Guterres.

Manufofin sun hada da kawo karshen talauci, kawo karshen yunwa, da tabbatar da samun makamashi mai sauki, daukar matakan gaggawa don yaki da sauyin yanayi, da kuma inganta daidaiton jinsi.

Wasu Shugabanni Kasashe A Taron UNGA Na September 22, 2022
Wasu Shugabanni Kasashe A Taron UNGA Na September 22, 2022

Wani rahoto na watan Yuli ya ce tasirin yanayin , da tasirin cutar COVID-19, da yakin Ukraine da kuma raunin tattalin arzikin duniya sun yi illa ga ci gaba da cimma manufofin ci gaban.

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden

Shugaban Amurka Joe Biden na daga cikin shugabannin kasashen duniya da Firai Ministoci da Sarakuna 145 da suka shirya yin jawabi a babban taron da za a fara ranar Talata. Ana sa ran Biden da Guterres duk za su ba da na nasu jawabin a ranar ta Talata.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron Lokacin G20 Summit A New Delhi September 10, 2023.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Lokacin G20 Summit A New Delhi September 10, 2023.

Shugabannin kasashen Britaniya, China da Faransa da kuma Rasha ba za su halarci taron ba, yayin da wasu manyan Ministoci ne za su wakilci kasashen.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy shi ma ya na shirin gabatar da jawabi a taron ranar Talata, da kuma halartar taron kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ranar Laraba.

Shugaban Ukraine Zelenskyy
Shugaban Ukraine Zelenskyy

Guterres ya ce zai gaya wa shugabannin cewa wannan ba lokaci ba ne na neman "matsayi ko gadara ba."

"Wannan lokaci ne da za a taru don samar da mafita na hakika," in ji Guterres. "Lokaci ya yi don sasantawa don kyautata al’amuran gobe."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG