Taron Koli na G20 A Australia.

Taron Kolin Shugabannin G20 A Australia.

Shugabanin kasashen da suke halarta taron kolin kungiyar G20 a Brisbane kasar Australia suna aiki akan shirye shiryen kara yawan aiyuka da kyayyakin da kasashe suke sarafawa, a yayinda shugaban Rasha Vladimr Putin yake barazanar cewa zai bar wurin taron tun ba' gama ba a saboda cacar bakin da ake yi akan hannu da Rasha take dashi a rikicin Ukraine.

Prime Ministan Australia Tony Abott ya kalubalanci mahalarta taron da su fito da takamamen shirin da za'a hada da asusun da aka kafa na dala biliyan biyu, da fatar samar da aiyukan yi da kuma karfafa gwiwar gudanar da harkokin kasuwancin da babu tsangwama.

Jaridar kasar Australia mai suna The Australian ya samu copin daftarin sanarwar bayan taro dake bayani cewa shugabanin kungiyar sun cimma daidaituwa wajen kokarin bunkasa tattalin arziki da kashi biyu da digo daya daga cikin dari.

Gobe Lahadi idan Allah ya kaimu za'a gabatar da sanarwar bayan taro
A harabar zauren taron, masu zanga zanga sun taru domin jawo hankalin mahalarta taron akan batutuwan da suka danganci rashin daidaito tattalin arziki, da yaki da cutar Ebola da kuma canin yanayi. Ya zuwa yanzu dai ba'a bada rahoton barkewar tarzoma ba.