A kalla mutum goma ne suka samu raunuka sanadiyyar wani tarzomar tsakanin Manoma da wasu Fulani makiyaya, bakin haure a wasu kauyuka na yankin karamar hukumar Bagwai, a jihar Kano Najeriya, kimanin kilomita 70 daga birnin Kano.
Wakilin muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari, yace a lokacin daya ziyarci, yankin ya samu dubban shanu, suna kiwo, yayin da jami’an tsaro, suke dakon ko takwana a gefe guda.
Bello Magaji Jarumawa,shugaban kungiyar Miyetti Allah, a yankin karamar hukumar ta Bagwai, yace wandannan Fulani, sun fito ne daga kasashen, Nijar, Chadi da Kamaru, yace kowane shekara suke zuwa.
Wani Manomi Ali Isiyaku Bagwai, yace makiyayan sun zo a lokacin da ba’a kauda hatsi ba suka nufi cikin gonaki, inda akayi sare-sare amma ba’a yi kisa ba.
Daya daga cikin Fulani Muhammad Bello, yace duk wanda yace an yimasa ta’adi karya ne, yakuma kara da cewa daga nan har Abuja zasu tafi, yana mai cewa Yobe, Jigawa, Katsina da Kaduna, duk akwai burtali, kasar kano ce kwai suka kashe burtali.
Muhammad Bello, ya bukaci Manoma da suyi hakuri, su ci gaba da aikin su, ya kara da cewa duk wanda aka tabawa dukiya, ya samu manyan su, ko da yake jami’an tsaron sun kama biyu daga cikin makiyayan da ake tuhuma da raunana ‘ya’yan Manoman.