Dakarun Sojojin Najeriya, dake fafatawa da ‘yan kungiyar Boko Haram na samu tallafi daga ‘yan civilian JTF, wato kato da gora da kuma ‘yan tauri, a yankin Gombi, dake arewacin, jihar Adamawa.
A gefe guda kuma an bukaci jama’a, dasu dukufa da adu’ar, samu nasarar, fatattakar ‘yan kungiyar, ta Boko Haram, ko jama’a zasu samu sa’ ida.
Shima shugaban hadakar matasa, na ;yan kato da gora, wato civilian JTF, Alhaji Bako Ali Gwani, yace lokaci yayi, da jama’a zasu tashi tsaye domin kare kansu.
Ya kara da cewa nan bada jimawa ba suna fatan kawo karshen, wani fafatawar da ake yin da ‘yan kungiyar Boko Haram, kuma suna fatan samun nasara.
Wani shugaban addini, Rev. A.M Gadzama, ya bukaci 'yan siyasar yankin da 'yan kungiyar, Boko Haram, suka addaba dasu dawo kusa da jama'ar su a dai-dai wannan lokaci da jama'ar ke bukatarsu.